Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Wakilai 180 a majalisar shura ta Iran, a cikin wata sanarwa, sun jaddada wajabcin neman fansar shahidan Iran da kawo ƙarshen fahimtar juna da ake yi da Amurka, suna masu yin alkawarin yin duk ƙoƙarin da zai yiwu don tsarawa da ɗaukar matakan a aikace don neman fansa.
Wakilan da suka sanya hannu a kan sanarwar, sun buƙaci shugabancin majalisar shura, da su kafa kwamiti na musamman nan take don sake duba tattaunawar da fahimtar juna, da kuma bin aiwatar da sharuɗɗan da jagoran juyin juya halin Iran ya kayyade.
"Matakin yaƙi ya shiga cikin yanayi mai tsanani, musamman bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, yaƙin ya ɗauki sabon salo bayan tsagaita wuta."
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa majalisar tana da niyyar sanya matakan shari'a a cikin ajandarta wanda ya haɗa da ƙarfafa rukunan tsaro na ƙasar, da amincewa da doka ta musamman don sarrafa mashigar Hurmuz.
Mambobin majalisar shura sun bayyana cewa, biyo bayan sanarwar shugaban Amurka Donald Trump na kawo ƙarshen yarjejeniyar fahimtar juna, ana sa ran shugabannin rassan gwamnati uku a Iran su bayyana matsayi mai ƙarfi na juyin juya hali game da wannan.
A cikin wannan batu sanarwar ta bayyana cikakken goyon baya ga ayyukan sojojin Iran, musamman wajen aiwatar da ikon Tehran a kan mashigar Hurmuz, tare da tabbatar da alkawarin wakilan na yin duk ƙoƙarin da suke iya don ba da tallafin da ake buƙata ga cibiyar soji.
"Yaƙi ya bayyana hakikanin manufar Amurka: sansanonin soji ta kafa su ne don kare muradun Amurka da 'Isra'ila,' ba ƙasashen da ke karbar bakuncin ba, inda al'ummar Jordan suka nuna kin amincewarsu ga manufofin Washington".
A yau ranar Talata, mai magana da yawun sojojin Iran, Birgediya Janar Mohammad Akrami-Nia, ya tabbatar da cewa sojojin Iran ba za su ja da baya ko kaɗan game da matsayinsu kan mashigar Hurmuz ba, yana mai jaddada cewa ba za a buɗe mashigar da yaƙi da ta'addancin Amurka ba.
Akrami-Nia ya kara da cewa mutunta haƙƙoƙin al'ummar Iran ita ce hanya ɗaya tilo ta buɗe mashigar Hurmuz, yana mai tabbatar da a lokaci guda cewa Iran tana da alhakin neman fansar jinin shahidai, musamman jagora shahidi.
Kwanakin da suka gabata sun shaida tashin hankali na ta'addancin Amurka a kan yankuna da cibiyoyin tattalin arziki a kudancin Iran, wadda ta mayar da martani ta hanyar kai hari a kan wurare da cibiyoyin Amurka masu muhimmanci a Tekun Farisa, kuma ta tunkari ƙoƙarin wucewar jiragen ruwa ba bisa ka'ida ba a mashigar Hurmuz.
Shin kuna ga ganin Hukumar Iran zata zartar da wannan bukatar kuwa?
Me ye ra’ayinku ga batun?
A ganinku mee ya hana Iran Daukar Fansa har zuwa yanzu?
……….
Your Comment